Jerin Lokuta da Jihohin da aka Taba ƙaƙaba wa Dokar Ta-ɓaci a Najeriya
Ayyana dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar Rivers ya sanya lissafin lokutan da wani shugaba ya ayyana irin wannan dokar sau biyar a faɗin ƙasar, tun bayan komawar Najeriya mulkin dimukraɗiyya a shekarar 1999.
BBC ta yi duba dangane da lokuta da jihohin da aka ƙaƙaba wa dokar ta-ɓaci ga kuma jerinsu:
1) Jihar Rivers 18 ga watan Maris 2025
A ranar Talatar 18 ga watan Maris na 2025 ne rikicin siyasa da ake fama da shi a jihar Rivers – wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa – ya kai magaryar tuƙewa, bayan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.
Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da ƴan majalisar dokokin jihar har na tsawon watanni shida sannan ya miƙa jihar ga Vice Admiral Ibokette Ibas mai ritaya a matsayin kantoma.
Wannan ya biyo bayan duk wasu matakan da aka ɗauka a baya domin sasanta rikicin, kamar yadda shugaban na Najeriya ya bayyana.
Siyasar jihar ta Rivers ta damalmale ne tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin gwamnan jihar Siminalayi Fubara da magabacinsa, ministan birnin tarayyar Najeriya, Nyesom Wike.
Lamarin ya kai ga cewa ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike sun yi barazanar tsige gwamna Fubara.
2) Borno, Yobe da Adamawa May 14, 2013
Read Also:
Sakamakon ƙara ƙamari da ƙungiyar Boko Haram ta yi wajen kai hare-hare a kan Musulmi da Kirista abin da ya nemi ya tayar da rikicin addini, shugaban lokacin Goodluck Ebele Jonathan ya ayyana dokar taɓaci a jihohin da hare-haren ƙungiyar suka fi yawaita da suka haɗa da Borno da Yobe da Adamawa.
To sai dai kuma saɓanin abin da ya faru a sauran dokokin na ta-ɓaci, Goodluck Ebele Jonathan bai dakatar da gwamnonin ba amma an aike da rundunoni daga gwamnatin tarayya sannan kuma an sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wuraren domin daƙile faruwar hare-hare.
3) Borno da Filato Disamba 31, 2011
A ranar ɗaya ga watan Disamban 2011, Shugaban Najeriya na lokacin, Goodluck Ebele Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci ta farko a kan wasu ƙananan hukumomin jihar Borno da na Filato sakamakon rikice-rikicen ƙabilanci da kuma na Boko Haram.
4) Jihar Ekiti Oktoba, 2006
Rikicin shugabanci a jihar Ekiti ya janyo shugaban Najeriya na lokacin, Cif Olusegun Obasanjo ƙaƙaba wa jihar dokar ta-ɓaci a watan Oktoban 2006.
Rikicin dai ya fara ne daga taƙaddamar tsige gwamnan jihar na lokacin, Ayo Fayoshe al’amarin da ya jefa jihar cikin ruɗani.
Obasanjo ya naɗa Birgediya Janar Adetunji Olurin mai ritaya a matsayin kantoman riƙo har zuwa lokacin da aka samu zaman lafiya.
5) Jihar Filato 18 ga Mayu 2004
A ranar 18 ga watan Mayun 2004, shugaban Najeriya na lokacin, Cif Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Filato, inda aka dakatar da gwamnan lokacin Josua Dariye da ƴan majalisar dokokin jihar.
Cif Obasanjo ya naɗa Manjo Janar Chris Alli mai ritaya a matsayin kantoman riƙo.
Shugaba Obasanjo ya ce ya ɗauki matakin ne bisa gazawar Josua Dariye daƙile faruwar rikicin da ya janyo zubar da jini a jihar tsakanin Musulmai da Kirista, al’amarin da ya janyo rasa rayuka fiye da 2,000 tun watan Satumban 2001.