Jihohin Najeriya 17 za su Fuskanci Ruwan Sama Kamar da Bakin Kwarya – NiMET

 

Abuja – Hukumar da ke hasashen yanayi a Najeriya, NiMET ta bayyana cewa wasu jihohin Najeriya za su fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Hukumar ta sanar da cewa akwai jihohin da ruwan ba zai yi karfi ba amma dai za a iya kwashe kwanaki uku ana tafka ruwan a jere.

Jihohin da ruwa zai yi karfi

Hasashen NiMET ya kuma nuna cewa za a yi kwarya kwaryan ruwan sama a kimanin jihohi 17 na Arewa, inji rahoton Daily Trust.

Sanarwar hukumar ta bayyana cewa za a tsula ruwan ne na kwanaki uku daga ranar Litinin, 23 ga watan Satumba har zuwa Laraba, 25 ga Satumbar 2024.

“Za a fuskanci ruwa mai karfi gami da tsawa a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihohin Neja, Nasarawa, Benuwai, Filato da Kwara.

“Da rana da kuma marece za a sha ruwa marar karfi a wasu sassan Kwara, Abuja, Neja, Benuwai da Kogi.”

A cewar NiMET.

Lokutan da ruwa zai sauka a jihohi

The Punch ta rahoto hukumar ta kuma ce a saurari zuwan ruwan sama a safiyar ranar Litinin a jihohin Sokoto, Kebbi, da kuma Borno.

Da yammacin ranar Litinin kuwa, NiMET ta yi hasashen ruwa zai sauka a jihohin Jigawa, Borno, Yobe, Taraba, Adamawa, Gombe, Bauchi, Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da Sokoto.

Hukumar ta yi kira ga wadanda ke zauna a garuruwan da ambaliyar ruwa ke masu barazana da su dauki matakan kare rayukansu.

An kuma shawarci matafiya musamman na sufurin jiragen sama da su nemi bayanan yanayi daga shafin hukumar domin kare kansu daga barazanar ruwa da iska.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here