Jihohin Najeriya da za su Fuskanci Ruwan Sama Hade da Tsawa a Kwanaki 3 – Nimet
Abuja – Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana hasashen saukar ruwan sama hade da tsawa a sassa daban-daban na kasar daga Lahadi zuwa Talata.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Asabar a Abuja, an nuna yiwuwar samun hadurra sakamakon iska mai karfi a Taraba, Adamawa da Kaduna ta Kudu.
NiMet ta yi hasashen ruwa da tsawa
NiMet ta ce za a samu ruwa hade da tsawa a jihohin Filato, Abuja, Nasarawa, Kwara, Neja da Kogi da hadari a Arewa ta Tsakiya, inji rahoton Punch.
A Kudu, an yi hasashen haduwar hadsari da safiyar Lahadi tare da yiyuwar hadari hade da tsawa a Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Delta.
Har ila yau, hukumar ta yi hasashen cewa za a iya samun ruwa hade da tsawa a wasu sassa na jihohin Anambra, Oyo, Edo, Imo, Abia, Ekiti, da sauransu.
Hasashen yanayin NiMet na ranar Litinin
A ranar Litinin, NiMet ta ce za a samu rana mai zafi a yawancin arewacin Najeriya, sannan za a iya samun ruwa hade da tsawa a wasu sassan Adamawa, Taraba da Kaduna da yamma.
Arewa ta Tsakiya kuwa za ta iya fuskantar zafin rana da kuma hadari da safiyar Litinin, sai kuma tsawa da yamma a jihohin Filato, Abuja, Benue, Kogi, Kwara da Nasarawa.
Read Also:
A kudu kuma, za a samu hadari hade da zafin rana, tare da yiyuwar tsawa a Akwa Ibom, Rivers da Cross River da safe, sannan hakan na iya faruwa a jihohin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas da Yamma.
Jihohin da ruwa zai sauka a ranar Talata
A safiyar Talata kuwa, NiMet ta ce za a samu hasken rana da dan hadari a Arewa, sai dai ana hasashen samun hadari mai hade da tsawa a Taraba da Yamma.
Za a kuma iya samun ruwa a Taraba, Adamawa da Kaduna. A Arewa ta Tsakiya kuwa, za a samu hadari da safe, da kuma tsawa da yamma a Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa da Abuja.
A Kudu, za a samu hadari da safe tare da hadari hade da tsawa a Cross River, Akwa Ibom da Lagos. Daga baya, za samu tsawa a Abia, Imo, Ebonyi, Anambra, Oyo, Edo, Delta da sauransu.
Hukumar NiMet ta ba ‘yan Najeriya shawara
NiMet ta shawarci jama’a su zauna a wurare masu iska da sanyi tare da shan ruwa sosai saboda zafin rana da ka iya janyo gajiya ko rashin lafiya.
Ta kuma shawarci jama’a su yi allurar rigakafin cutar sankarau, su rika wanke hannu akai-akai, guje wa cunkoso da saka takunkumi, da nisantar masu fama da cututtuka.
Haka kuma ta bukaci jama’a su guji fitowa daga rana daga karfe 12:00 na rana zuwa 3:00 na yamma, su kuma kula da guguwar da ka iya tasowa kafin zuwan ruwa.
Hukumar ta bukaci kamfanonin jirgin sama su rika tuntubar NiMet domin samun rahoton yanayi na filin jirgi kafin tashinsu.