Jita-Jitan Harbe Iyan Zazzau ba Gaskiya Bane – Shehu Iya Sa’idu
Wani dan rikon Iyan Zazzau ya karyata jita-jitar da ake yadawa ta cewa kashe marigayin aka yi.
Yaron wanda ya kasance Tafidan Dawakin Zazzau ya ce jita-jitar da ake yadawa ta kisan mahaifin nasa ba ta da wani asali ballanta tushe.
A yau Asabar, 2 ga watan Janairu ne aka binne marigayin a Sabon Gari.
Dan rikon marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya yi watsi da jita-jitan da ke yawo na cewa kashe marigayi yariman Zazzau wanda ke shari’a da gwamnatin jihar Kaduna kan zabar sarkin Zazzau na 19 aka yi.
Legit.ng ta samu labarin rasuwar Aminu a jihar Lagas a safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu.
An dauki gawarsa zuwa Sabon Gari, jihar Kaduna, a ranar Asabar inda aka yi sallar jana’izarsa a masallacin Juma’ar da ke yankin kafin aka binne shi a gidansa.
Read Also:
Jim kadan bayan sanar da labarin mutuwarsa a Kaduna a ranar Juma’a, sai jita jita ya fara yawo a jihar cewa an kashe marigayi yariman a Lagas lokacin da fito daga gidansa don zuwa mallaci don sallar Asubahi a ranar Juma’a.
Sai dai da yake zantawa da jaridar Daily Trust bayan binne marigayin, Shehu Iya Sa’idu wanda ke rike da mukamin Tafidan Dawakin Zazzau kuma dan marigayi Iyan Zazzau ya ce jita jitan kisan bai da tushe.
Ya kara da cewa kasancewarsa daya daga cikin makusantan marigayin, yana iya tabbatar da cewa mutuwar Allah marigayin yayi.
“Ya yi fama da rashin lafiya, amma saboda shi mutum ne mai jarumta, mutane da dama basu san da hakan ba face mu da muke kusa da shi,” in ji shi.
“Jita jitan harbi ba gaskiya bane kuma ina daya daga cikin makusantanshi saboda mahaifina ne ya rike shi sannan shima ya rike ni tun ina shekaru biyu.
“Don haka ina iya fada maku cewa lokacinsa ne yayi kuma Allah Ubangiji wanda ya bamu shi ya karbi abinsa. “Addu’anmu shine Allah ya yi masa rahama sannan ya bashi Alhannah Firdausi,” in ji shi.