Daga Ranar da Jonathan ya Koma APC ya Gama Zubar da Ragowar ƙimarsa – Dr Nwodo
Jigon babbar jam’iyyar hamayya ta ƙasa PDP ya gargaɗi Jonathan kan shirin komawa APC mai mulki.
Dr Okwesilieze Nwodo, wanda tsohon shugaban PDP ne yace zai matukar bakin ciki idan Jonathan ya sauya sheka.
Yace da zarar tsohon shugaban ya koma APC duk wata ƙima da mutuncinsa zai zube a idon yan Najeriya.
Abuja – Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Dr Okwesilieze Nwodo, ya gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kada yayi gangancin komawa jam’iyya mai mulki APC, kamar yadda Leadership ta rawaito.
Nwodo ya bayyana cewa matukar Jonathan ya koma APC to ya zubar da ragowar mutuncinsa da kimarsa a idon yan Najeriya.
Yace tsohon shugaban ba zai iya kawo sauyi a jam’iyyar ba domin komawarsa zata ƙara shagwaba yan APC ne su cigaba da ɗaukar abinda duke yi dai dai ne.
Dakta Nwodo ya yi wannan maganar ne yayin da yake zantawa da kafar watsa labarai ta Arise Tv.
Duk wanda ya koma APC ya fara dana sani
Read Also:
Jigon jam’iyyar hamayya ta ƙasa PDP ya ƙara da cewa duk wanda ya fice daga PDP ya koma APC kan kowane dalili ya fara dafa keya yana dana sani.
A cewarsa babu wani abun da zaka ji dadi ko kayi murna a jam’iyyar APC kuma yace ba zai ji ɗaɗin ganin Jonathan a APC ba.
Wani sashin jawabinsa yace:
“Shawarata ga Jonathan kada ya kuskura ya afka duk wani daɗin baki da tarairayar da ake masa ya koma APC. Daga ranar da ya shiga APC ya gama zubar da ragowar ƙimarsa.”
“Wannan itace shawara ta gareshi domin babu mutanen da suka ci mutuncinsa a matsayinsa na shugaban ƙasa kamar jam’iyyar APC, me zai sa ya shige ta? Shin yana tunanin gyara abinda aka lalata ne idan ya koma APC? Ba zai yuwu ba.”
Wace jam’iyya ce zata iya ceto Najeriya?
Mista Nwodo ya ce PDP ce kaɗai zata iya zuwa madafun iko ta sassaita komai da APC ta lalata kuma ta ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta yau.
Yace:
“Mutum ɗaya tilo da zai iya zuwa ya ceto Najeriya daga halin ƙaƙanikayi da ta tsinci kanta yau ƙarƙashin APC shine shugaban ƙasa a karkashin PDP.”
“Goodluck Jonathan babban abokina ne, mun yi aiki tare, zan yi matukar bakin ciki idan ya sauya sheka zuwa APC, bansan mai zai yi a can ba.”