Zaben 2023: Kungiya a Arewacin Najeriya ta Bayyana Jonathan a Matsayin Wanda ke da Kwarewa Wajen Tafiyar da Lamuran Kasar

 

Wata kungiya a arewacin Najeriya ta nuna goyon bayanta ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabannin babban zaben 2023.

Kungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin wanda ke tarin kwarewa wajen tafiyar da lamuran kasar.

A cewar kungiyar, Jonathan ya rigada ya san yadda abubuwa ke gudana don haka shugabancin kasar ba zai zame masa bakon abu ba.

Abuja – Wata kungiyar siyasar arewa mai suna Northern League of Professionals ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya fi cancanta don dorewar damokradiyyar Najeriya da kuma kawo ci gaba a kasar.

Kungiyar ta ce idan har aka sake ba Jonathan damar shugabantar kasar, zai kai ta ga matakin ci gaba ta hanyar karfafa nasarorin da aka samu a wannan gwamnati mai ci.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran kungiyar, Alhaji Mohammed Yusuf Ajiji, jaridar The Sun ta rahoto.

Wani bangare na sanarwar ta ce:

“Gwamnati ci gaba ce kuma ita ce ta kai ga gwamnatin Buhari ta ci gaba da kammala wasu ayyuka da aka fara a karkashin Jonathan.

“Ayyuka kamar ginawa da gyara hanyoyin jiragen kasa, gadar Neja ta biyu, gadar Loko-Oweto, titin Legas zuwa Ibadan da dai sauransu duk gwamnatin Buhari ce ta aiwatar da su duk da cewar sun fara aiki ne a karkashin Shugaba Jonathan.

“Wannan misali ne na ci gaba a gwamnati kuma za mu so ganin yanayi inda Shugaba Goodluck Jonathan zai ci gaba daga inda shugaban kasa Buhari ya tsaya domin tabbatar da ganin cewa akwai wadataccen abubuwan more rayuwa da aiwatar da manufofi da tsare-tsare domin magance matsalolin da kasar ke fuskanta. Manufarmu ita ce tabbatar da samun ci gaba mai dorewa ta hanyar ci gaba da aiwatar da shirin ba tare da katsewa ba.”

Kungiyar ta bayyana Jonathan a matsayin zakarar gwajin dafin tabbatar da dimokradiyyar Najeriya wand aba za a taba mantawa da shi ba, wanda ya aiwatar da sauye-sauye da dama a harkokin zaben kasar tare da mika mulki ga abokin hamayyarsa a cikin lumana wanda ba a taba tsammani ba a Afirka.

Alhaji Alajiji ya ce duk cikin masu neman takarar shugaban kasa, babu wanda ke da tarin kwarewa kamar Jonathan wanda ya yi aiki a matsayin malamin jami’a, mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban kasa.

Ya ce Jonathan ne yafi dacewa don hada kan kasar a wannan mawuyacin lokaci da ake da koe-koke daban-daban a fadin kasar, rahoton Inependent.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here