Komawa APC: Goodluck Jonathan ya yi Magana Kan Jita-Jitar

 

Dr Goodluck Ebele Jonathan, tsohon shugaban Nigeria ya karyata jita-jitar cewa ya koma jam’iyyar APC.

A ranar Laraba ne wata rahoto ta rika yawo a dandalin sada zumunta da ke cewa Jonathan ya koma APC don ya yi takara a 2023.

Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan ya ce rahoton ba gaskiya bane ya kara da cewa mai gidansa ya dukufa wurin yin wasu ayyukan.

Tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Ebele Jonathan ya musanta cewa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki a kasar, SaharaReporters ta rawaito.

A ranar Laraba, wani rahoto ya bazu a dandalin sada zumunta cewa tsohon shugaban kasar ya nuna sha’awar yana son ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Rahoton ya kara wa jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar yana da shirin sake fitowa takarar shugaban kasa a 2023 karfi.

Mai magana da yawun Jonathan ya ya karyata rahoton

Amma a martaninsa, Ikechukwu Eze, mai magana da yawun Jonathan ya ce rahoton labarin kanzon kurege ne.

Eze ya ce:

“Rahoton ba gaskiya bane. Idan ya sauka sheka zuwa wata jam’iyyar. Za a sanar ta kafar da ta dace.”

Ya jadada cewa mai gidansa bai nuna alama ko niyyar komawa jam’iyyar APC mai mulki ba.

Ya kara da cewa:

“Mutumin nan fa yanzu akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da suka shige masa gaba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here