APC ta Bayyana Cewa za ta Dauki Mataki Kan ‘Ya’yan Jam’iyyar da Suka kai Karar ta Gaban Alkali

 

Uwar APC za ta hukunta wadanda suke kai karar Jam’iyya gaban Alkali.

Wani jigon jam’iyyar yace sun gaji da surutu, za su fara daukar matakai.

APC NEC ta umarci ‘ya ‘yan jam’iyya suyi sulhu a gida, a guji zuwa kotu.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APC za ta dauki mataki mai tsauri a kan ‘ya ‘yanta da suka saba wa umarnin da aka bada na yin sasanci, suka je kotu.

Jaridar Punch tace jam’iyyar APC mai mulki za ta dauki mataki a kan duk wadanda suka shigar da kara a maimakon a zauna ayi sulhun cikin-gida.

Wani daga cikin manyan jam’iyyar a Abuja ya shaida wa jaridar cewa za a dauki wannan mataki.

Za a ga aiki da cika wa

A cewar wannan babba da ba a bayyana wanene shi ba, jam’iyyar APC za ta dauki mataki a kan masu saba mata a maimakon ta cigaba da ja masu-kunne.

“Mun tashi daga yin barazana, za mu fara daukar mataki.”

Uwar jam’iyya za ta dauki matakin da bai saba tsarin mulkinta ba. Za a karfafa wa shugabannin jam’iyya da ke jahohi su hukunta duk masu kunnen-kashi.

“A matakin jam’iyya na kasa muna tattara wadanda suka saba doka da abubuwan da suka faru. An ba reshen jam’iyya na jaha karfi su dauki matakin da ya dace, wanda ya zo daidai da doka da tsarin jam’iyyar APC.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here