Bayan Kashe Matafiya: Hukumar Gudanar da Jarabawa ta Jami’ar Jos ta Dakatar da Rubuta Jarabawar Zangon Karatu na Biyu 2019/2020

 

Hukumar gudanarwa ta jami’ar Jos ta dakatar da ci gaba da gudanar da jarabawa zangon karatu na na biyu na shekarar 2019/2020 cikin gaggawa bayan barazanar tsaro da ya dunfaro a jahar Filato, The Nation ta ruwaito.

Sanarwar da Mataimakin Magatakarda, Abdullahi Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa:

“Bayan barkewar rashin tsaro da ya faru a wasu sassan garin Jos, wanda ya sa Gwamnatin Jahar Filato ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Jos, Karamar Hukumar ta Arewaci, hukumar gudanarwar Jami’ar Jos ta amince da dakatar da jarabawar zangon karatu na biyu na 2019/2020.

“Sakamakon haka, an dakatar da duk jarabawar da aka shirya tsakanin Litinin 16 zuwa Asabar 21 ga Agusta 2021 har sai an samu sabuwar sanarwa.”

Ya kara da cewa:

“Ana sanar da dukkan Dalibai na Jami’ar da ke zaune a dakunan kwanan dalibai da su kasance a cikin dakunan kwanan su da kuma gujewa motsin da ba dole ba kamar yadda hukumar gudanarwa ke aiki ba dare ba rana tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da Gwamnatin Jahar Filato don tabbatar da cewa an kare rayuka da dukiyoyin membobin Jama’ar Jami’ar musamman dalibai.

“An kuma shawarci daliban da ke zaune a wajen makarantar da su kasance a gida a wannan lokacin.” Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here