Jos: An Tsinci Gawawwaki a Tafkin Laminga
An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke jihar Jos, inda aka kai su asibitin koyarwa na jihar.
Ana zargin gawawwakin mutanen da suke tsoron jami’an tsaro su damkesu a kan satar da aka yi a gidan Dogara ne
Dama a ranar Asabar da ta gabata ne bata-gari suka yi sata a gidan tsohon Kakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara An tsinci gawawwaki 4 a tafkin Laminga da ke jihar Filato, Jos, jaridar Newswire ta wallafa.
Read Also:
Jaridar Daily Trust ta bayyana hakan, inda tace gawawwakin mazauna wurin ne wadanda suka fada cikin tafkin ne don gudun kada jami’an tsaro su kama su a makon da ya gabata a matsayin wadanda suka yi sata a gidan tsohon sanata, Yakubu Dogara, a Jos.
A ranar Lahadi da safe ne wasu bata-gari suka balle gidan tsohon Kakakin majalisar dattawan, inda suka kwashe tsadaddun abubuwa daga gidan. A ranar Lahadin da ta gabata ne aka sanya wa mazauna Jos kullen awanni 24 a jihar, bayan sun balle ma’adanar gwamnati da ke Dogon Dutse a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar. Bayan saka kullen ne aka yi ta sace-sace a ma’adanan gwamnatin Jos da Bukuru, inda suka kwashi kayan abinci.
Omini Bridget, jami’ar hulda da jama’a ta asibitin koyarwa da ke Jos, ta tabbatar da tsintar gawawwakin guda 4 a tafkin bayan kawo su asibitin. Amma wata majiya daga wuraren Laminga ta ce gawawwakin da aka tsinta guda 8 ne, an kai wasu gawawwakin wasu asibitocin ne daban.