Adadin Mata Masu Juna-Biyu Waɗanda ke Fuskantar ƙarancin Abinci Mai Gina Jiki ya ƙaru da Kashi 25 cikin 100 – MDD

 

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce adadin mata da ‘yan matan da ke da juna-biyu waɗanda ke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 a ƙasashe matalauta kamar Somaliya da Habasha da kuma Afghanistan.

UNICEF ya ƙiyasta cewa fiye da mata da ‘yan mata biliyan ɗaya a sassan duniya na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Asusun ya bayyana cewa matsalolin da aka shiga a duniya shekaru biyu da suka wuce ciki har da yaƙe-yaƙe da kuma annobar Korona su ne suka ƙara ta’azzara shigar mata cikin ƙangin yunwa.

UNICEF ya buƙaci ƙasashen duniya da su sanya batun samar da isasshen abinci a duniya a dukkan farkon lamuransu da kuma taimaka wa shirye-shiryen samar da abincin da suka gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here