Kotu ta yi Umarni da a yi wa Abduljabbar Kabara Gwajin Kwakwalwa

 

Wata kotun Musuluncin da ke shari’ar Malamin addinin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da kunne a wani zaman ci gaban shari’ar da ake yi masa a birnin Kano da ke arewacin kasar.

Kotu ta bayar da umarnin ne bayan Malamin addinin Musuluncin ya gaza amsa tambayoyin da alkalin kotun Mai Shari’a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa ranar Alhamis.

Ranar Juma’a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jahar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Tun da misalin karfe 9:20 na safe ne aka soma zaman kotun da ke Kofar Kudu daura da gidan Sarkin Kano tare da gabatar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan wanda ake zargi.

Lauyoyin da ke kare Abduljabbar karkashin jagorancin Barista Sale Bakaro sun soki yadda ake tsawaita shari’ar da kuma sabbin tuhume-tuhumen da aka gabatar kan Malamin.

Sai dai Alkali Sarki Ibrahim Yola ya ce a fahimtarsa wadannan tuhume-tuhume da aka gabatar wajibi ne domin a karantawa wanda ake zargi laifukan da ake bukatar amsa daga gare shi.

Hakan ne ya sa kotu ta amince a karanta wa wanda ake ƙara sabbin tuhume-tuhumen da ake masa – domin ya musanta ko ya amince da su.

Wannan matsayi na alkali bai yi wa lauyoyin Abduljabbar dadi ba inda suka ce idan aka ci gaba da tafiya a haka to za su daukaka kara.

Yadda zaman kotu ta kaya

Da farko Alkalin ya gabatar da tambayoyi uku ga Sheikh Abduljabbar sai dai bai amsa ko guda daga ciki ba.

Tambaya ta farko ita ce: “Ranar 10 ga watan 8 a shekara ta 2018 Abduljabbar a unguwar Sani Mainagge a karatunka na Jauful Fara inda ka yi wa Annabi SAW kage na cewar a Hadisi na 1365 da na 1358 na sahihi Muslim cewa Annabi SAW fyade ya yi wa Nana Aisha, wanda hakan ya saba wa 382 (b) kundin tsarin shari’ar Musulunci ta 2000.”

Sai dai Abduljabbar bai amsa wannan tambayar ba dalilin da ya sa kotu ta tambaye shi wanne yare yake ji, amma nan ma bai ce uffan ba.

Kotu ta ci gaba da yi masa tambaya har sau uku amma bata samu kowanne amsa daga Abduljabbar ba.

Tuhuma ta biyu: “Ranar 10 ga watan 8 2018, a karatunka na Jauful fara ka yi amfani da kalaman ɓatanci inda ka yi masa kage kan aurensa da Ummu Safiya, ka ce Sahihi Muslim ya ce Annabi ya kwace wa wani mutum matarsa 1365, wanda hakan cin zarafi ne, laifi ne da ya saba wa sashe na 382(b)”

An sake tambayar Abduljabbar ko ya fahimci abin da ake tuhumarsa da aikatawa amma ya yi shiru. Alkali ya sake tambaya: “Shin ka yarda ka aikata laifi ko ba ka yarda ba?”

Abduljabbar ya yi shiru bai ce komai ba.

Tuhuma ta uku: “A ranar 10 ga watan 8 ta shekarar 2019, a darasinka na 93 ka yi amfani da kalaman ɓatanci cewar dole manzon Allah ya yi wa matarsa Safiyya ya aureta, wanda babu wannan hadisi kai ka kirkire shi. Kuma hakan ya saɓa wa sashe na 382 (b) na kudin tsarin Shari’ar Musulunci na Kano na 2000.”

Kan wannan tambayar Abduljabbar ya yi gum da bakinsa.

Tuhuma ta hudu: “A darasinka na 90 da na 98 na karatun Juful fara ga kaga wa Annabi laifin zina, inda ka ce wata mata ta nemi Annabi ya biya mata bukatarta, kuma ka ce ya yi hakan, wannan ya saɓa wa sashe na 382 na kundin hukunta laifuffuka na shari’ar Musulunci na 2000 ta jahar Kano.”Alkali Sarki Yola ya sake tambayar Abduljabbar kamar farko amma ya yi shiru bai ce uffan ba.

Yadda hukunci ya kasance

Alkali Sarki Yola ya ɗage sauraron shari’ar bayan gabatar da waɗannan tuhume-tuhume ba tare da samun amsa daga wanda ake zargi ba.

Sai dai ya bayar da umarnin bincikar lafiyar Sheikh Abduljabbar saboda rashin amsawa kotu tambayoyin da ta yi masa tare da wata takardar zuwa ga likitan kunne da ke asibitin Kwararru na Murtala, domin yin gwajin.

Daga nan ya ɗage zaman shari’ar zuwa mako biyu za a dawo kotu ranar 16 ga watan Satumbar 2021 domin ci gaba da shari’ar. Ya kuma umarci a bai wa lauyoyin wanda ake kara kwafin shari’ar domin daukaka karar da suke bukata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here