Bayan Dakatar da Shi: Sheikh Abduljabbar Kabara ya Mayarwa da Gwamnatin Jahar Kano Martani

Shaikh Abdul Jabbar Kabara ya yi martani kan dakatarwa da gwamnatin Kano ta yi masa.

Shaihin malamin cikin tattaunawar da aka yi da shi ya ce zaluntarsa gwamnatin ta yi domin ba ta bashi damar kare kansa ba.

Abdul Jabbar Kabara ya ce kwamishinan ilimi na jihar Kano shi kansa ya fadi cewa abinda aka yi masa zalunci ne.

Babban malamin ya ce tunda yanzu an hana shi karatu zai mayar da hankali wurin yin rubuce-rubuce da za su hana wadanda suka zalunce shi ‘yin barci’.

Babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa’azo da gwamnatin jihar ta yi “zalunci ne”, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jahar.

Gaza hana shi yin taron da ya yi a makon da ya gabata na daga cikin dalilan da yasa gwamnatin da zartar da wannan hukuncin a kansa a cewar shaihin malamin.

“Kwamishinan ilimi ya yi magana da madadin gwamnati cewa ana zaluntar Abdul jabbar ne sannan abubuwan da malaman nan suke yi ba su da su gaskiya ko kadan, sun shigar da siyasa ne a cikin addini,” a cewar babban malamin.

Abduljabbar ya ce wannan kalaman na kwamishinan ilimi na cewa ana zaluntar sa kawai ya isa raddi ga gwamnati cewa abinda ta yi zalunci ne.

Ya kara da cewa malaman da ke zaluntar sa sun sauka daga turbar ilimi sun koma amfani da siyasa domin cimma manufar da suka saka a gaba.

Da aka masa tambaya a kan matakin da zai dauka, shaihin malamin ya ce, babu batun cigaba da karatu a yanzu sai dai zai yi amfani da lokacin sa domin rubuce-rubuce wanda za su ‘hana wadanda suka zalunce shi barci”.

Da aka masa tambaya game da batun zargin batanci ga sahabban Anabbi Muhammad SAW, shaihin malamin ya ce ba a ji ta bakinsa ba ballantana a zartas da hukunci game da hakan.

Kazalika, ya ce shi kokarin kore batanci ya ke yi ga addinin musulunci tare da hujojoji kwarara ba neman tada rikici ko zaune tsaye ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here