Kada Gwamnati ta Matsa wa Jama’a Kan Rigakafin Cutar Corona – Sarkin Musulmai

 

Sarkin musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar III ya shawarci gwamnati da kada ta takura wa jama’a akan riga-kafin cutar COVID-19.

A cewarsa, matukar ana son a samu nasara, wajibi ne malaman addini da shugabannin gargajiya su hada kai wurin wayar wa jama’a kai akan ta.

Ya kara da cewa, jama’a da dama za su kirkiro labaran bogi da karairayi akan riga-kafin, ta hanyar wayar da jama’a kawuna ne kadai za a samu nasara.

Sarkin Musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar III, a ranar Laraba ya shawarci gwamnati da kada ta matsa wa ‘yan Najeriya akan riga kafin COVID-19.

Ya bayar da wannan shawarar ne yayin da yake jawabi a wani taro na limamai da malaman addini akan COVID-19 wanda aka yi a Abuja, Vanguard ta wallafa.

Sarkin ya bayar da shawarar kada a takura wa ‘yan Najeriya don su amince da riga-kafin, amma a dinga ilimantar da su da kuma basu bayanai masu kyau akan cutar.

Kamar yadda yace: “Ya kamata a dinga zama ana tattaunawa da mutane don a fahimtar dasu amfanin yin allurar ga lafiyarsu, daga nan za su amince. Ba wai a takura musu ba.

“Lokacin da Allah ya kai ni wannan matsayin a 2006, ana tsaka da neman yadda za a yi riga-kafin cutar polio.

“A lokacin, ministan lafiya, Farfesa Babatunde Osotimehin ya tunkareni da maganar don mu fahimtar da mutane.

Anan na amince saboda muna son mu ga mutane cikin koshin lafiya.”

“Haka muka samu shugabannin gargajiya daga jihohin arewa 19 da Abuja, a haka muka shirya kwamitin shugabannin gargajiya na polio.

Kuma kwamitin ya yi aiki kwarai, yanzu haka shekaru 13 kenan da aka magance cutar. “Wannan yana daya daga cikin amfanin shugabannin gargajiya.

Amma shugabannin gargajiya ba za su iya yin irin wannan wayar da kan ba kamar shugabannin addini. “Duk wani basarake da baya da kusanci da malaman addini ba mutumin kwarai bane.

Sakamakon hadin kai da malaman addini ne ya janyo nasarar kawar da cutar polio.” Yace.

A cewarsa, za a wallafa labaran kanzon kurege akan riga kafin COVID-19, sakamakon karancin ilimi akanta, don haka wajibi ne a wayar da kan jama’a.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here