Muhimmin Sakon da Babban Sarkin Ife, Adeyaye Ogunwusi ya Aikawa ‘Yan Siyasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin Jahohin Oyo da Ondo da kuma shugaban majalisar saraukan kabilar Yoruba.

Babban sarkin masarautar Ife, Adeyeye Ogunwusi, ya ce sun ziyarci Buhari ne akan al’amuran da suka shafi tsaro.

Da yake magana da manema labarai bayan ganawarsu da Buhari, Basaraken ya gargadi ‘yan siyasa akan cakuda batun tsaro da siyasa.

Adeyeye Ogunwusi, babban sarkin masarautar Ife ta kabilar Yoruba, ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan batun tsaro a kasa.

Da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da Buhari, Basaraken ya ce ziyarar tana da nasaba da al’amuran da suka shafi tsaro a yankin kudu maso yamma.

Babban sarkin ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji cakuda batun tsaro da siyasa tare da bayyana cewa yin hakan shine yake haddasa asarar rayuka.

“Shugaban kasa ya bamu tabbacin cewa ba za’a saka siyasa a sha’anin tsaro ba. Akwai balagurbin mutane a kowanne yanki na kasar nan kamar yadda muke da su a yankin kudu maso yamma.

“Na ziyarci shugaba Buhari ne a matsayina na shugaban majalisar sarakunan kabilar Yoruba domin samun tabbacinsa cewa babu wani bangare da zai saka siyasa a batun kalubalen tsaro a yankin kudu maso yamma,” a cewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here