Muna ƙaddamar da Sababbin Hare-hare a Babbann Birnin Iran, Tehran – Isra’ila

 

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana ƙaddamar da wasu sababbin hare-hare a babbann birnin Iran, Tehran.

Kafofin yaɗa labarai na Iran sun bayar da rahotannin fashewa a wurare daban-daban a Tehran din.

Tun da farko Iran dai ta harba makamai masu linzami a kan Isra’ila, inda aka riƙa jin ƙarar jiniya ta ankararwa a arewaci da tsakiyar, Isra’ilar.

Makamai masu ‘ya’ya da sauran tarkacen bam sun yi illa a wurare da yawa a tsakiyar Isra’ila – amma kuma babu rahoton jikkatar mutane.

Iran ta yi gargadin cewa za ta rufe mashigar Hormuz gaba daya muddin Amurka ta aiwatar da barazanar Shugaba Trump ta cewa zai shafe gaba dayan tasoshin samar da lantarki na Iran

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here