Kaduna: Muhimmancin Taron Cika Shekara 50 da Kafa Gidan Tarihin a Jahar

 

  A wannan Asabar din cibiyar bincike da ajiye kayayyakin tarihin wato Arewa House da ke Kaduna ke bikin cika shekaru hamsin cur da kafuwa.

Ana saran shugabanni siyasa da Sarakuna da sauran masu ruwa tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar su halarci taron.

An dai kafa cibiyar ta Arewa a gidan Sardauna da nufin kiyayye tarihin Arewacin Najeriya tare da bai wa masu tasowa damar ganin yadda yankin ya zauna a dunƙule.

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Architect Muhammad Namadi Sambo wanda zai jagoranci taron, ya shaida wa BBC cewa a kullum cibiyar na gudanar da abubuwan da za su kara ƙulla zumunci da tuna baya da ci gaban arewa da ma ƙasar baki-daya.

Tabbatar da haɗin-kai na daga cikin ayyukan cibiyar kuma irin wannan taro na taka rawa sosai da karfafa zumunci da hadin-kai da kuma ci gaban Najeriya, in ji Architect Namadi Sambo.

Sannan ya ce mutane irinsu marigayi Sardauna ne suka aza tubalin da a yau Najeriya ke kai na ci gaba. Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce lura da yadda al’ummar Najeriya ke karuwa a kullum haka ma bukatu na karuwa shi yasa ake mata kallon ba ta wani samun ci gaba.

“Daya daga cikin muhimman hanyoyin da Sardauna ya taimaka shi ne samar da ilimi kyauta, domin sai dai ilimi ake samun wanzuwa, akwai bukatar kowanne dan arewa ya dage wajen neman ilimi.”

Architect Namadi, ya kara da cewa kowacce gwamnati na nata ƙoƙari kawai dai hidindimu ne da bukatu ke karuwa a ko da yaushe shiyasa ake yawan samun ƙorafi.

Takaitaccen tarihin Ahmadu Bello Sardauna

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na ɗaya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma ɗane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Ɗan Fodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya naɗa shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka naɗa shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da ya yi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.

Ya kuma halarci ƙasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zaɓe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya ƙasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam’iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaɓen da aka gudanar bayan samun ƴancin kai.

Bayan kammala zaɓe, ya zaɓi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya naɗa Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Firaminista.

Ya taka rawa sosai wajen haɗa kan yankin Arewacin ƙasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban ƙasa.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji ƴan kabilar Ibo suka jagoranta

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here