Gwamnan Jahar Kaduna ya Fadi Dalilinsa na Rage Ma’aikata a Jaharsa

 

Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi fashin bakin kan dalilin rage ma’aikata a jaharsa.

El-Rufai ya ce kudaden da gwamnatin jihar ke kashewa wurin biyan albashi ya yi wa jahar yawa, bayan albashin ba a samun kudin yin wasu ayyukan.

Gwamnan ya ce ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa ne ke cinye fiye da kashi 90 cikin 100 na kudin jahar.

Rashin adalci ne mutanen da ba su kai 100,000 ba su rika cinye fiye da kashi 90 na cikin kudin jahar yayin da sauran wadanda ba ma’aikatan gwamnati ba su morar komai Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya yi bayanin abin da yasa gwamnatinsa ke rage ma’aikata a jahar.

Ya ce hakan ya zama dole ne domin jahar ba ta da kudin da za ta cigaba da yi wa mutane ayyuka gami da yawan albashin da ta ke biya a lokacin da kudaden da gwamnatin tarayya ke bawa jahohi duk wata (FAAC) bai karu ba.

Gwamnan ya ce kudin da jahar ke samu daga gwamnatin tarayya, FAAC, tun tsakiya shekarar 2020 kamar sauran jahohi, da kyar ya ke isa a biya albashi ballantana a yi wasu ayyukan.

Ya ce wannan aikin rage ma’aikatan zai shafi masu rike da mukaman siyasa inda ya ce an yi hakan ne domin rage kudaden da ake kashewa.

El-Rufai ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin ta bakin mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye.

Ya ce: “A Nuwamban 2020, abin da ya rage wa gwamnatin Kaduna bayan biyan albashi shine N162.9m. A wannan watan jahar ta samu N4.83bn daga FAAC sannan ta biya albashi da N4.66bn.”

Bayanin ya nuna watannin da suka biyo baya kusan lamarin bata canja zani ba wato dai da an biya albashi babu wani kudin da jahohin za ta yi wasu ayyukan da su.

Gwamnan ya ce bai kamata jaha da ke da ma’aikatan gwamnati kasa da 100,000 su rika lakume fiye da kashi 90 cikin 100 na kudaden jahar, su bar wa sauran da ba ma’aikatan gwamnati bane ko masu rike da mukaman siyasa kaso kalilan.

“Wannan rashin adalci ne ‘yan tsiraru su rika cinye kaso mafi tsoka na kudin jahar.

“Ma’aikatan gwamnati na da muhimmanci don haka ya kamata a kayyade dai-dai adadin da ake bukata.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here