Gwamnatin Kaduna ta Gabatar da Kasafin Kudin 2022 ga Majalisar Dokokin Jahar
Gwamnatin jahar Kaduna ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga majalisar dokokin jahar.
 Gwamnan ya bayyana yadda gwamnati ta tsara kashe kudaden a bangarori daban-daban na rayuwa.
 Gwmanan ya kuma mika godiya ga majalisar dokokin bisa goyon bayan da suke bashi a mulkinsa.
Kaduna – Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 233 ga majalisar dokokin jahar Kaduna a yau Talata 12 ga watan Oktoba.
Kasafin kudin yana dauke da bayanin kashe Naira biliyan 146 a fannin ayyuka da jari da kuma na Kashewa akai-akai da suka kai Naira biliyan 87.6 a shekarar.
El-Rufa’i ya yi nuni da cewa rabe-raben da aka yi a cikin alkaluman kasafin kudin na shekarar 2022 sun yi nuni da kimar siyasa da ka’idojin shugabanci wanda a koda yaushe suke jagorantar kasafin kudi shida na baya da gwamnatinsa ta gabatar.
El Rufa’i ya ce alkaluman shekarar 2022 sun yi kasa da kasafin kudin 2021 na N237.52bn, wanda ke da N157.56bn na ayyuka da jari da kuma N79.96bn da aka tsara don kashewa akai-akai, kashi 66% zuwa 34% na jarin da ake samu.
A sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar a shafinta na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da aka sa a gaba na kasafin 2022 sun hada da Ilimi, Kiwon Lafiya da Kayayyakin more rayuwa, kamar dai na kasafin baya.
Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga majalisar dokokin jahar bisa goyon baya da suke ba gwamnatinsa da ta dukufa wajen ayyukan ci gaba da al’ummar jahar ta Kaduna.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here