Hukumar Kwastam ta Bayyana Yadda ‘Yan Fasa ƙwaurin shinkafa ke Tallafawa ‘Yan Bindiga a Katsina
Hukumar kwastam (NCS) ta bankaɗo sirrin yadda yan sumoga ke kaiwa yan bindiga man fetur a jahar Katsina.
 Shugaban hukumar, Wada Chedi, yace da farko sun fara samun bayanan sirri amma daga bisani suka bi diddigin lamarin har suka tabbatar.
 A cewarsa yan sumoga na ƙara wa tankin mai girma sannan su cikashi a gidan mai sukai wa yan bindiga.
Katsina – Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) reshen jahar Katsina ta bayyana cewa yan fasa ƙwaurin shinkafa na yin zagon ƙasa a yaƙin da ake da yan bindiga a Katsina.
 Wada Chedi, muƙaddashin kwanturolan kwastan na jahar, shine ya bayyana haka a wata fira da manema labarai a ofishinsa ranar Litinin da yamma.
Premium times ta rawaito shi yana cewa yan sumoga na taimakawa yan ta’addan wajen tsallake matakan da gwamnatin jahar ta ɗauka.
Yan sumoga na kaiwa yan bindiga fetur
 Mista Chedi ya bayyana cewa masu aikin sumoga sun nemo sabbin hanyoyin kaiwa yan bindiga kayayyakin abinci da sauransu.
Yace yan fasa gwaurin na amfani da manyan tankuna domin ɗaukar man fetur su kaiwa yan ta’addan a cikin jeji.
Yace:
 “Kwanan nan, mun kama motocin Peugeot 504, waɗanda yan sumogan suka kirkiri sabbin tankunan man fetur kuma suka cikasu taf da mai.”
 “Yan fasa kwaurin suna zuwa gidajen man fetur suna cika waɗannan tankunan, sannan su siyarwa yan bindiga.”
Taya kwastam suka samu nasarar gano haka?
A cewar Chedi, hukumar kwastam ta fara samun bayanan sirri kan irin wannan ayyukan da yan fasa kwaurin suka fara. “Mun fara samun bayanan sirri, daga nan muka sa musu ido tun daga inda suke siyan man fetur ɗin har zuwa inda suke siyarwa yan bindiga.”
“Amma suna fahimtar ashe mun biyo su, domin suna da wayo, nan take suka bar motocin suka tsere, muka kwace motocin.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here