Gwamnatin Kaduna ta Hana Sare Itatuwa a Kananan Hukumomi 7 na Jahar
Gwamnatin Jahar Kaduna ta hana yawon gararamba da shiga dazuka domin sare itatuwa a kananan hukumomi bakwai.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun da Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru.
Gwamnatin Jahar Kaduna ta ce an dauki matakin ne domin inganta tsaro kuma ta duk wanda aka kama yana saba dokar zai fuskanci doka.
Gwamnatin Jahar Kana ta haramta yawon ‘gararamba’ a gari da shiga manyan dazuka a jahar domin yin ayyuka, The Cable ta rawaito.
Jahar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jahar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jahar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Read Also:
Aruwan ya ce an bada sanarwar ne bayan gwamnatin ta gana da kungiyar masu sayar da itatuwa, katako, da gawayi a jahar.
Kananan hukumonin da dokar ta shafa?
Ya lissafa kananan hukumomin da abin ya shafa kamar haka, Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru.
Sanarwar ta ce:
“Domin inganta tsaro ga kowa a jahar, bayan samun shawarwari daga hukumomin tsaro, gwamnatin jahar Kaduna ta dakatar da sare bishiya don katako, girki, gawayi da wasu harkokin cinikayya a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Chikun, Giwa, Kachia, Kauru da Kajuru nan take.
“An kuma hana dukkan yawon gararamba da ayyuka a manyan dazukan da suke kananan hukumomi bakwai da aka lissafa, dokar ta fara aiki nan take.”
Aruwan ya shawarci mazauna jahar da su guji aikata abubuwan da aka hana yana mai cewa hukumomin tsaro za su tabbatar an bi dokar.
A watannin baya-bayan nan an ta sace mutane da kai hare-hare a jahar Kaduna.