‘Yan Bindiga Sun Kaiwa Asibiti Hari  a Jahar Bayelsa

 

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu fashi da makamai ne sun kai hari asibitin gwamnati na jahar Bayelsa a ranar Talata.

Sakamakon harin, sun sace duk wasu kudade da tsadaddun abubuwan likitocin da suke kan aiki da na marasa lafiya.

Ana zargin ‘yan fashin sun shiga asibitin ne bayan sun fasa katangar asibitin ta baya sannan wani jami’in tsaron asibitin ya ce wannan ne hari na biyu.

Bayelsa – Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai farmaki asibitin gwamnati na jahar Bayelsa, Diete Koki Memorial Hospital, inda suka sace duk wasu kudade da tsadaddun abubuwan likitoci da marasa lafiya.

Asibitin yana kan titin Opolo ne a Yenagoa, babban birnin jahar, Daily Trust ta rawaito.

Lamarin ya faru ne da safiyar Talata. Ana zargin ‘yan fashin sun fasa katangar bayan asibitin ne sannan suka shiga ciki.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, daya daga cikin likitocin da suke kan aiki, Dr Okeleghel Awudumapu, ya sanar da manema labarai cewa ‘yan fashin sun kai farmakin ne lokacin yana dakin likitoci.

A cewarsa, sai da suka kwashe masa duk wasu kayan tagomashi da kuma na marasa lafiya sannan suka tsere.

Shugaban asibitin, Dr Emmanuel Fetepigi, bayyana aikin a matsayin kauyanci.

A cewar Dr Fetegi, hukumar asibitin da ma’aikatar lafiya ta kasa za su tabbatar sun yi iyakar kokarin ganin irin wannan lamarin bai sake aukuwa ba.

Wani jami’in tsaron asibitin, Mr James Benini, ya ce wannan shine karo na biyu da aka taba kai wa asibitin farmaki.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jahar, SP Asinim Butswat, ya yi tsokaci dangane da lamarin ya ce:

Har yanzu ba a kawo mana rahoto ba. Amma na tura DPO Ekeki don ya nemo bayanai a kan lamarin daga asibitin.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here