Dalilin da Yasa Gwamnatin Jahar Kaduna ta Kwashe Dalibanta Daga Jos

 

Duba da yadda rikici a Jos yake kara ta’azzara, gwamnatin jahar Kaduna ta kwashe dalibai ‘yan asalin jahar Kaduna a Filato.

Wannan na zuwa ne bayan barkewar rikici a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya kai ga sanya dokar hana fito a wasu sassan jahar.

Gwamnatin jahar Kaduna ta bayyana cewa, wannan wani yunkuri ne na kubutar da daliban daga fadawa rikicin dake faruwa.

Kaduna – Gwamnatin jahar Kaduna a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta ta sanar da kwashe ‘yan asalin jahar wadanda daliban jami’ar Jos ne da sauran manyan makarantun jahar Filato, Punch ta rawaito.

Wannan ya biyo bayan yawaitar kashe-kashe a garin Jos ta Jahar Filato da sake sanya dokar hana fita a wasu sassan jahar.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da tallafin karatu da bashi na jahar Kaduna, Malam Hassan Rilwan, wanda ya sanar da hakan, ya ce an kammala kwashe daliban a karshen makon da ya gabata.

Ci gaban, in ji shi, ya yi daidai da umarnin gwamnatin jahar cewa ya kamata a kwashe dukkan daliban jahar Kaduna da suka makale saboda yanayin tsaro a jahar Filato.

A cewarsa, Jami’an tsaro karkashin kulawar hukumar sun kwashe dalibai 87 a ranar Juma’a, 20 ga Agusta, 2021, inda ya kara da cewa tuni aka sake sada daliban da danginsu.

Rilwan ya ce Hukumar za ta ci gaba da kasancewa cikin kwazo a cikin irin wannan yanayi mai rikitarwa tare da bai wa ‘yan kasa tabbacin jajircewar gwamnati na kare rayukan daliban jahar a Jahar Filato da sauran wurare.

Rilwan ya kara da cewa: “Hukumar ta kuma lura da goyon bayan da ta samu daga Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Uba Sani wanda ya taimaka matuka wajen kwaso daliban.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here