Bayan Tsige Inuwa: Majalisar Dokokin Kaduna ta Rantsar da Sabon ɗan Majalisa Mai Wakiltar Mazabar Sabon Gari
Kakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Yusuf Zailani, ya bada rantsuwar kama aiki ga sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Gari.
Honorabul Ali Baba ya zama ɗan majalisa ne biyo bayan zaɓen cike gurbi da ya gudana a mazabar Sabon Gari a watan Yuni.
Majalisar Kaduna ta bayyana kujerar da babu kowa saboda kin halartar harkokin majalisa da tsohon mai wakiltar yankin ya yi.
Kaduna – Kakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani, ya rantsar da sabon ɗan majalisa, Alhaji Usman Ali-Baba, na jam’iyyar PDP ranar Alhamis, kamar yadda Leadership ta rawaito.
Ali Baba shine sabon ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Gari, a majalisar dokokin jahar Kaduna.
Read Also:
Legit.ng Hausa ta gano cewa sabon ɗan majalisan ya lashe zaɓen maye gurbi, wanda ya gudana ranar 20 ga watan Yuni, 2020 a faɗin mazaɓar Sabon Gari.
Ida zaku iya tunawa an gudanar da zaɓen cike gurbin ne biyo bayan bayyana kujerar ɗan majalisan yankin da babu kowa da majalisar dokokin Ƙaduna ta yi a watan Afrilu.
Meyafaru da ɗan majalisa na farko?
Majalisa ta bayyana kujerar da babu kowa ne saboda gazawar tsohon ɗan majalisa mai wakilatar yankin, Aminu Shagali, wajen shiga harkokin majalisa har na tsawon kwanaki 360.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan rantsar da shi, Ali Baba ya godewa Allah (SWT), kakakin majalisa, mambobin majalisa, da kuma jam’iyyar PDP.
Hakazalika ya godewa al’ummar mazaɓar Sabon Gari, bisa ganin cancantarsa da kuma amince masa ya wakilce su a majalisar dokokin jahar.