Kaduna: ‘Yan Sanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu Daga Hannun Su
An ceto mutane 23 da suka hada da kananan yara da mata wanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a wata musayar wuta a Jihar Katsina.
Yan bindiga shida aka kashe yayin musayar wutar tare da gano dabbobin da suka sace da kuma babura harma da bindiga.
Kakakin yam sandan jihar ya bayyana cewa sun yi wa yan bindigar kawanya bayan sun sami labarin gaggawa na harin da suka kai kauyen Lambo a Kurfi.
An kashe yan bindiga da ba su gaza shida ba a wata musayar wuta tsakanin su da jami’an tsaro ranar Talata a karamar hukumar Kurfi da ke jihar Katsina, Vanguard ta ruwaito.
An ruwaito cewa mutane 23 da suka hada da mata da kananan yara wanda yan bindigar suka yi garkuwa dasu lokacin da suka kai hari kauyen Lambo a karamar hukumar Kurfi suma an ceto su yayin barin wutar.
Read Also:
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce yan bindiga da suka haura 30, suna harbe harbe a iska da bindigun AK 47, suka kai hari kauyen tare da kashe mutane biyu da yin garkuwa da mutane 23 (mata 17 da kananan yara 6).
SP Isah ya ce samun labarin jami’an tsaro ke da wuya suka shiga fafutuka tare da yiwa yan bindigar kawanya wanda ya yi sanadiyar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da dabbobin da aka sace.
A cewar sa, “da misalin karfe 2:30 na ranar Talata, yan bindiga da yawan su ya haura mutane 30, suna harbe harbe a iska, suka kai hari kauyen Lambo, mazabar Wurma, karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, sun kashe mutum biyu tare da garkuwa da mata 17 da kananan yara 6.
“Jami’an yan sanda, sojojin sama da na kasa duk sun samu masaniya kuma sun toshe duk wata hanya da zasu iya guduwa.
“Haka zalika, jami’an sun yi yan bindigar kawanya a tsakanin kauyen Ummadau zuwa Kwayawa kuma aka yi musayar wuta, lamarin da ya janyo mutuwar yan bindiga 6, ceto duka mutane 23 da akayi garkuwa da su, an gano shanu 23, tumaki 20, da kuma akuyoyi 31 tare da kwace babura 12 da bindiga guda daya kirar G3.
“Hukumomi na ci gaba da bincike don kama ragowar bata gari ko kuma gano gawarwaki.
“Ana ci gaba da bincike,” SP Isah ya bayyana