An Kaiwa Hukumar EFCC Korafi Kan Hukumar NERC
A yayin da ‘yan Nigeria ke tsaka da kukan karin kudun wutar lantarki, sai ga shi an bankado badakala a hukumar NERC.
Wani dan kishin kasa ya rubuta takardar korafi zuwa hukumar EFCC tare da sanar da ita yadda manyan jami’ai suka yi watanda da biliyoyi a NERC.
Hukumar NERC ce ke kula da rarraba wutar lantarki da kuma kayyade farashin kudin wuta da ‘yan kasa zasu biya.
Dai-dai lokacin da yan Najeriya ke korafin ƙarin kuɗin wutar lantarki, sai ga shi ana zargin kwamishina da membobin hukumar rarraba wutar lantarki (NERC) da rabawa kansu biliyoyin Naira a matsayin albashi ta barauniyar hanya.
Read Also:
Gidan jaridar na Premium Times ya samu wata takarda da aka aikewa Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) da wani ɗan kishin Najeriya ya rubutawa kokensa akai.
A cikin takardar korafin, Sam Amadi, ya bayyana wasu kwamishinoni guda bakwai da suka raba Naira miliyan 75 kowannensu wanda adadin ya haura miliyan 525 domin sayan manyan motoci masu tsada kawai.
Mai korafin, Amadi, ya bayyana rashin gwamsuwarsa na rabawa Kwamishinonin miliyan 75 kowannensu.
Bayanai daga wasu majiyar ya nuna an yi amfani da kudin ne don shigo da motocin alfarma daga Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Takardar korafin ta ce, “Duk motocin an sayo su kuma an yi musu rijista da sunayen wadannan kwamishinoni”.
A Cewar rahoton, ya nuna shugaban hukumar ta NERC na karɓar albashi sama da Naira miliyan 83.4 abinda ya saɓa da wanda doka ta sahale masa na miliyan 59.9 kamar yadda kuma hukumar NERC ta yarje.