Kakakin Majalisar Bauchi ya yi Martani Kan Canza Jam’iyya

 

Ba za a samu gagarumin sauyin sheka na wani babban dan siyasa ba a Bauchi kamar yadda ake ta hasashe a wasu bangarori.

Hakan ya fito ne daga kakakin majalisar dokokin jihar wanda ya karyata cewar yana shirin barin jam’iyyar APC mai mulki.

A cewar Abubakar Suleiman, rahoton barinsa jam’iyyar ba komai bane face jita-jita.

Abubakar Suleiman ya ce baya shirin barin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa wata jam’iyya kamar yadda ake ta rade-radi a wasu bangarori.

Suleiman wanda ya kasance kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya fayyace hakan ne lokacin da shugabannin jam’iyyar suka kai masa ziyara gidansa.

Da yake daukar alwashin biyayya ga APC, Suleiman ya bukaci shugabannin da su yi watsi da jita-jitan cewa zai bar jam’iyyar.

Ya yi magana kan rigimar da ya biyo bayan kamfen din jam’iyyar a zaben cike gurbi da aka yi kwanan nan a karamar hukumar DSS inda aka zarge shi da kin yin magana.

Ya ce akwai yarejeniya kan Shugaban masu rinjaye a majalisar yayi magana a madadin yan majalisa na APC, The Nation ta ruwaito.

Ya ce:

“Ina baku tabbacin cewa ni dan APC ne. Babu wanda zai cire ni daga jam’iyyar.

“Wasu mutane na cewa ban je Dass don zabe ba, amma hatta takwarotina sun san cewa ban ji dadi ba a ranar Juma’a harta kai ban iya halartan sallar Juma’a ba.Shugaban masu rinjaye da wasu mambobi sun je chan don wakiltanmu.

“Mafi akasarin jita-jitan nan mutane da suka dogara kan bata suna, karya da raba kan siyasa don samun kudi ne ke yada su.

“Wasun su basu manta da abunda ya wakana ba a lokacin rantsar da mu, wanda suke kallo a matsayin rashin yi wa jam’iyya biyayya. Amma yan majalisar APC sun yafi junansu sannan sun ci gaba. Me zai sa suma ba za su yafe ba sannan suyi aiki tare da mu don sake gina jam’iyyarmu? Idan har sun damu da ci gaban jam’iyyar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here