ALLAH ya yi wa Kakar ‘Dan Takarar Gwamna na NNPP a Jihar Kano Rasuwa

 

Kakar dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta rasu.

Za a yi jana’izar Hajiya Mowa Sufi Yakasai a fadar mai martaba sarkin Kano bayan sallar Juma’a.

Marigayiyar ta rasu bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya, tana da shekaru 103 a duniya.

Kano- Allah ya yiwa Hajiya Mowa Sufi Yakasai, kakar dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, rasuwa.

Hajiya Yakasai, wacce ke da shekaru 103 a duniya ta rasu bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Za a yi jana’izarta a fadar mai martaba sarkin Kano bayan sallar Juma’a, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Daga cikin ‘ya’yanta akwai tsohon sakataren ilimi na kwalejin karatun Musulunci da shari’a na Aminu Kano (AKCILS), Ibrahim Abubakar Aminu.

Ta rasu ta bar yara da jikoki da yawa wadanda a cikinsu harda wani likita a babban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Dr Atiku Musa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here