Watsa Kalaman Kiyayya da Tunzura Jama’a na da Illa ga Kasa – Lai Mohammed ga Shugabanni

 

Gwamnatin Najeriya roki shugabanni da cewa, ya kamata su zama masu wanzar da zaman lafiya.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan yada labarai da al’adu a Najeriya, Alhaji Lai Mohammed.

Lai Mohammed ya lura cewa, a kasar an samu shugabannin da ke watsa kalaman kiyayya da tunzura mabiyansu.

Cape Verde – Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin siyasa da na addini da su daina “fitar da kalaman kiyayya” da za su iya cinnawa kasar wuta, TheCable ta rawaito.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, neya yi wannan gargadi yayin da yake zantawa da NAN a ranar Laraba 1 ga watan Satumba a tsibirin Sal, Cape Verde.

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, ministan ya je Cape Verde ne don halartar taro karo na 64 na hukumar kula da yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya (UNWTO) a Afirka da kuma bugu na biyu na dandalin saka hannun jari na duniya na UNWTO.

Da yake magana a gefen taron na duniya, ministan ya kuma gargadi kafafen yada labarai, musamman gidajen watsa labarai, da su bi ka’idar watsa labarai da sauran ka’idojin da aka gindaya musu.

A cewarsa:

“A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, kasar ta kasance mai ban tsoro, musamman a kafofin watsa labarai, tare da maganganun da ke haifar da tashin hankali lamarin da ya haifar da fargaba a Najeriya.”

“Kalaman kiyayya da ke fitowa daga bakin ‘yan siyasa, shugabannin addini da wasu gungun masu ra’ayi na da karfin da za su iya cinna wa kasar wuta.

A cewar ministan, wasu kalaman na ingiza wata kabila kan wata ko kuma wani addinin kan wani.

Ya kara da cewa:

“Babban shawararmu ga masu ruwa da tsaki shi ne ya kamata su fahimta kuma su tuna cewa shugabanci yana da nauyi da yawa, su rage kalaman kiyayya saboda suna da illa ga kasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here