Masarautar Kaltungo ta Yabawa Kungiyoyi Kan Tallafawa Masu-Bukata-ta-Musamman da Kekuna 250
Masu bukata ta musamman a masarautar Kaltungo a yau sun wayi gari cikin farin ciki a fadar Uban Kasa Mai Kaltungo Engr. Saleh Muhammad Umar OON (Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) a yayin da yake mika kekuna masu kafa uku uku wanda yawansu yakai guda 250 wanda kungiyar Community and Rural Life Enhancement Initiative (CREI) tare da hadin gwuiwar Beautiful Gates Handicapped People’s Center, Jos suka bayar ta hannun Uban Kasa.
Read Also:
Shugabannin kungiyoyin biyu Amb. Evang. Bitrus Caleb Dasar da Rev. Ayuba Gufwan sunyi duba da irin kokarin Uban kasa Mai Kaltungo wajen taimakawa don yaki da kwayar cuta ta Shan Inna a masarautar Kaltungo dama kasa gaba daya. Babu shakka wannan nasara da’aka samu wajen kawar da kwayar cutar Shan Inna a kasa Najeriya nasarace wanda ta samu tareda gudunmawar Uban kasa wajen wayar da kan al-umma don karbar allurar rigakafi na cutar Shan Inna
Uban kasa Mai Kaltungo ya bayyana farin cikinsa akan wannan namijin kokari da zaban masarautan Kaltungo daya daga cikin masarauta data ci gajiyar wannan tallafi. Uban kasa ya yabawa kungiyar akan wannan aiki nata na alheri tareda jawo hankulan masu hannu da shuni, kungiyoyi dama gwamnatoci da cewa suyi koyi da wadannan kungiyoyi.
Taron ya guduna ne a filin wasa na Olusegun Obasanjo dake cikin garin Kaltungo wanda yasamu halattar manya manyan masu sarautu a masarautar Kaltungo da yan’siyasa.