Benjamin Kalu ya yi Martani Akan Furucin Wani Dan Majalisar PDP

 

Majalisar wakilai ta nisanta kanta daga kira ga fara shirin tsige Shugaba Buhari.

Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar ya ce kiran da Kingsley Chinda na PDP yayi ba daidai bane.

Kalu ya bukaci yan Najeriya da kada su bari dan majalisar na PDP ya batar da su .

Majalisar wakilai ta yi watsi da bukatar wani dan majalisa na neman a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerar mulki.

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Obio/Akpor ta Jihar Rivers, Kingsley Chinda shine yayi wannan kira, inda ya bukaci yan Najeriya da su matsa lamba don ganin wakilansu a majalisar sun fara shirin tsige shugaban kasar a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun majalisar, Benjamin Kalu a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, ya ce kiran da dan majalisar na Peoples Democratic Party (PDP) yayi baya bisa ka’ida, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kalu ya zargi Chinda da kokarin amfani da kira ga tsige shi don daburta ziyarar da Shugaban kasar ke shirin kai wa majalisar.

Kiran ɗan majalisar da cewa “ra’ayin mutum ɗaya ne kawai daga cikin jam’iyyar adawa.

“Da a ce wannan kiran bayan zuwan Buhari majalisa ne kuma ya gaza yin cikakken bayani ko kuma ya ƙi ɗaukar shawararmu, sai a ce kiran ya yi ma’ana,” in ji Benjamin Kalu cikin wata sanarwa.

A cewar jaridar The Guardian, Kalu ya ce ya kamata ayi watsi da furucin dan majalisar na PDP.

Ya bukaci yan Najeriya da su yi hakuri su jira sakamakon ganawar da ake shirin yi tsakanin Buhari da mambobin majalisar wakilan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here