Kashe Matafiya Musulmai: Sojojin Najeriya Sun Kama Mutane 20 da Ake Zargi
Rundunar sojojin Najeriya a jahar Filato sun cafke wasu mutune 20 da ake zargi da kashe matafiya musulmai.
Wannan ya zo ne bayan da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa matafiya kisan gilla a wani yankin jahar ta Filato.
A halin yanzu, rundunar ta ce tana kan bincike don tabbatar da adalci da kuma mika su ga inda ya dace.
Jos, Filato – A baya, rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jahar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jahar, in ji rahoton PM News.
Read Also:
A sabbin rahotanni da suka shigo a yau kuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane 20 ne ya zuwa yanzu a cafke da hannu wajen kisan musulmai 25 a wani yankin jahar Filato.
Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.
Wani yankin sanarwar ya shaida cewa:
“Wadanda aka kama a halin yanzu suna tsare don amsa tambayoyi.”
Takwa ya ce Kwamandan rundunar, Maj-Gen. Ibrahim Ali, ya bukaci jama’a da su ba da sahihan bayanai masu sahihanci wadanda za su kai ga cafke sauran wadanda ake zargi, a halin yanzu.
Ya ce, kwamandan ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu, su kasance masu bin doka da oda kuma su ci gaba da ayyukansu ba tare da wani fargaba ba.
Hakazalika, ya ce jami’an tsaro sun kara kaimi wajen sintiri a cikin garin Jos don wanzar da zaman lafiya da tsaro.