Kada ku Dubi Matsayin Mutum, ku kama Duk Wanda ya zo Belin Masu Laifi – Muhammad Bello ga Hukumomin Tsaro

Ministan Abuja, Mallam Muhammad Bello, ya bukaci hukumomin tsaro kar su duba matsayin mutum, da ya zo belin me laifi su damƙe shi.

Ya ce sun samu rahoton cewa wasu manyan mutane na zuwa suna saka baki a saki masu laifi, ba zasu yarda haka ta cigaba da faruwa ba.

Ministan ya roki al’umma su taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan duk wanda suka ga ya kuɓutar da me laifi.

Abuja – Ministan babban birnin tarayya Abuja, Muhammed Bello, ya buƙaci hukumomin tsaro su cafke duk wanda ya zo neman a ba shi beli wani mai aikata manyan laifuka.

Ministan ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a wurin taron mako-mako da ake shirya wa Ministoci don bayanin ayyukan su, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Bello ya bayyana cewa yin hakan wani ɓangare ne a kokarin da suke yi wajen tsaftace birnin tarayya daga aikata manyan laifuka.

Ministan ya kuma ƙara da cewa harajin da ake karɓa a babban birnin tarayya wato Abuja, ana tsammanin nan gaba zai zarce wanda jihar Legas ke tarawa.

Mallam Muhammed Bello ya sanar da cewa a yanzun Birnin ya na tattara biliyan N200bn shekara-shekara daga karɓan Haraji, kamar yadda Punch ta rawaito.

Wane mataki gwamnati ke ɗauka kan tsaron Abuja?

Da yake jawabi kan matakan kawo karshen aikata manyan laifuka a Abuja, Ministan ya ce ya zama wajibi su ankarar da jami’an tsaro saboda sun sami rahoton yadda manyan mutane masu matsayi ke zuwa kubutar da masu laifi.

Ya kuma yi kira ga mazauna Abuja su tona asirin duk wanda ke kokarin kubutar da masu laifi ta hanyar kai rahotonsu ga hukumomin tsaro.

Bello ya koka cewa a halin yanzun gidan gyaran hali uku da ke Abuja duk sun cika taf kuma ba za’a ƙara ko mutum ɗaya da aka kama da laifi ba.

A cewarsa, idan Kotu ta tabbatar da laifin wani a Abuja sai dai a tura shi zuwa Gidan Yarin Suleja a jihar Neja, yayinda FCT ke shirin samar da Yari na musamman da za’a rinka ɗaure kananan yara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here