An Gudu ba a Tsira ba: An sake Kama Bursunonin da ‘Yan Daba Suka Saki a Jihar Edo

 

  Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Edo a kudancin Najeriya ta kama fursuna 10 daga cikin waɗanda suka tsere daga gidajen yari a Benin, babban birnin jihar.

  ‘Yan daba sun saki fursuna kusan 2,000 bayan sun fasa gidan yari biyu a Benin yayin zanga-zangar EndSars da aka gudanar a jihar.

  Shida daga cikin fursunonin an sake kama su ne da laifin fashi, yayin da aka kama ɗaya da laifn yunƙurin kashe wani da ya bayar da shaida a kotu a kansa.

  Jaridar Daily Trust ta ruwaito jami’an tsaro na cewa fursunonin na cikin mutum 126 da aka damƙe da laifin satar kayayyakin abinci a wuraren ajiya da dama a jihar.

   Yayin da yake nuna wa manema labarai waɗanda ake zargin, Kwamishinan ‘Yan Sanda Johnson Kokumon ya ce an kama mutum 28 da zargin wawashe rumbun ajiya na hukumar Kwastam, 45 da laifin yashe wata cibiyar lafiya, 13 da laifin sata a kamfanin Olam, 16 da laifin sata a Dorisday.

 Sai dai wasu daga cikin waɗanda aka kama ɗin sun musanta zargin sata da ake yi musu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here