Batanci ga Annabi(S.A.W): An Kama Ɗaliban da Suka Kashe Ɗalibar Kwalejin Ilimin Shehu Shagari

 

A yau ne wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta inda wasu matasa suka kashe tare da kone wata daliba a Sokoto.

Lamarin ya faru ne sakamakon zargin dalibar da rubutun batanci ga manzon Allah SAW a shafin yanar gizo.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sanda ta kamo wasu mutane biyu da ake zargin suna daga cikin wadanda suka yi aika-aikan.

Jihar Sokoto – Akalla mutane biyu ne aka kama bisa laifin kashe wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana a ranar Alhamis, Channels Tv ta rawaito.

A cewar rundunar ‘yan sandan, an zargi Deborah Samuel, ‘yar matakin mataki na biyu a kwalejin, da yin wani rubutu a dandalin sada zumunta wanda ya nuna batanci ga manzon Allah (SAW).

Rundunar ‘yan sandan ta ce daliban un dauki matashiyar da karfin tsiya daga wurin jami’an tsaro da hukumomin makarantar, suka kashe ta tare da konata Kurmus.

Wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu maza suke jifanta da sanduna tana kwance a kasa sanye da kaya mai launin ja.

Wasu faifan bidiyo sun kuma nuna wata wuta da ta tashi yayin da wani mutum ya fuskanci kyamara, yana mai cewa ya kashe ta kuma ya kone ta, yana kuma rike da kwalin ashana.

Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin cewa za ta gano wadanda aka gani a faifan bidiyon da aka yada a shafin Twitter, kuma za a kamo su nan ba da dadewa ba, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sanda a Sokoto, Sanusi Abubakar ya sanya wa hannu.

A cewar Malam Abubakar, an rufe makarantar tare da tura karin jami’an ‘yan sanda yankin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here