Jami’an Amotekun Sun Kama ‘Dan Kungiyar Asiri da ya Harbi Kansa
Jami’an hukumar Amotekun na Jihar Ogun sun kama wani Janai Sunday wanda ake zargi dan kungiyar asiri ne.
An kama Janai ne a cikin wani daji da ke hanyar kauyen Obada-Owode, karamar hukumar Imeko-Afon, Ogun bayan ya harbi kansa a hannu cikin tsautsayi.
David Akinremi, shugaban Amotekun na Imeko-Afon ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce karar harbin bindigan yasa suka shiga daji suka kamo wanda ake zargin a wurin da suke taro.
Wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne ya harbi kansa a yayin da ya ke kokarin ciro masakar harsashi daga cikin wata bindiga kirar pistola a jihar Ogun.
Lindaikeji ta rahoto cewa Janai Sunday ya harbi kansa a hannu, a cewar hukumar tsaro ta Amotekun reshen jihar Ogun.
Bindigar “Pistol ta fashe bisa tsautsayi, hakan yasa ya samu munanan rauni a hannunsa na hagu,” a cewar rundunar.
Read Also:
Yadda aka kama wanda ake zargin
Kwamandan Amotekun na Ogun, CP David Akinremi (murabus), ya ce Jinai Sunday da wasu ‘yan kungiyar asiri ta Aiye’ suna wurin taronsu a wani daji da ke kan hanyar Kauyen Obada-Owode, karamar hukumar Imeko-Afon na Jihar Ogun ne a lokacin da abin ya faru.
A cewar Akinremi, bayan jin karar harbin bindigan, shugaban Amotekun na Imeko-Afon, bayan samun bayannan sirri, ya tura jami’ansa suka kama wanda ake zargin da wani Adejare Kehinde. Shugaban na Amotekun ya ce a yayin da ake musu tambayoyi, ta bayyana cewa Adejare Kehinde ne ya ke siyo musu bindigu a Jamhuriyar Benin.
An yi nasarar kama wani Ogundele Elijah, wanda aka fi sani da Ogun 07, wanda ya bayyana cewa ya taba zuwa gidan yarin Ilaro ya yi wata shida saboda laifin shiga kungiyar asiri, saboda bayannan da aka samu daga wadanda aka kama da farko.
Jami’an na Amotekun sun ce suna cigaba da bibiyan sauran yan kungiyar.