Nassarawa: Anyi Nasarar kama Dan Ta’addan da ya Kashe Shugaban APC

 

A ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, aka wayi gari da samun labarin yin garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa, Philiph Schekwo.

Jim kadan bayan samun labarin sace shi, sai ga shi rahotanni sun sanar da cewa an tsinci gawarsa.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Talata, 1 ga watan Disamba, ya sanar da cewa an kama dan ta’addar da ya kashe Schekwo har gida.

An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya kashe Cif Philip Tatari Shekwo, shugaban jam’iyyar APC a jihar Nasarawa, kimanin sati biyu da suka gabata.

A ranar Talata ne Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanar da cewa ‘yan sanda sun kama dan ta’addan a garin Lafia, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Majiyoyi sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun zo gidan marigayi Schekwo da ke kan titin Kurikyo kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a garin Lafia da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare 11pm inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ƙarar harbin bindigun ne suka tashi marigayi Schekwo daga barci, inda nan take ya gano cewa akwai matsala, kuma take ya fara kiran lambobin wayar hukumomin tsaro amma basu ɗaga ba har aka ƙwamushe shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here