Jimoh Aremu ya yi Martani Akan Albashin ‘Yan Majalisa
Olaifa Jimoh Aremu ya ce ana yin karya game da albashin ‘Yan Majalisa.
A cewar Hon. Olaifa Jimoh, babu wani ‘Dan Majalisa da ke samun N10m.
‘Dan Majalisar ya ce ana yi masu karya da cewa albashinsu ya fi na kowa.
‘Dan majalisar wakilan tarayya, Olaifa Jimoh Aermu, ya karyata maganar cewa ‘yan majalisar tarayya suna tashi da mahaukacin albashi a Najeriya.
Daily Trust ta rahoto ‘dan majalisar na jihar Ogun yana cewa babu wani ‘dan majalisa dake samun Naira miliyan 10 a matsayin albashinsa kowane wata.
Jimoh mai wakiltar mazabar Egbado ta Arewa da Imeko Afon a majalisar tarayya ya ce mutane suna kara gishiri kan albashin da su da Sanatoci ke karba.
A cewar Hon. Olaifa Jimoh Aremu, N36m da N25m da ake cewa sanatoci da ‘yan majalisar wakilai suna samu a duk watan Duniya, ba gaskiya bane.
Read Also:
‘Dan majalisar jam’iyyar hamayyar ya bayyana wannan ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, 2020, wajen yaye wasu matasa da ya dauki nauyin horaswa.
‘Dan majalisar tarayyar ya dauki dawainiyar koya wa mata da matasa 400 daga jihar Ogun ta yamma, sana’o’i domin su samu su iya rike kansu nan gaba.
Haka zalika Olaifa Jimoh Aremu ya ce babu gaskiya a maganar da ake yi na cewa duk Dunia babu ‘yan majalisar dake samun albashi irin na Najeriya.
Jimoh bai bayyana abin da yake karba duk wata ba, sai dai ya bada shawara ga masu bukatar wannan su tuntubi ma’aikatar dake da alhakin kasafta albashi.
‘Dan majalisar ya ce ana yi masu karya kan abin da suke samu ne domin a bata masu suna.
Saboda irin wannan surutu ne kwanakin baya muka kawo rahoto game da albashin shugabannin Najeriya da su ka hada da’yan majalisun tarayyan kasar biyu.
Kamar yadda wata takarda da ta fito daga ma’aikatar ‘RMAFC ta nuna, albashin shugaban majalisar dattawan Najeriya a shekara shine N8,694,848:75 (N8.69m).
Zuwa yanzu, albashin shugaban majalisar tarayyar a kowane wata ya tsaya ne a kan N722,570:72.