An Kama Wasu Bata Gari Masu kwacen wayoyin Salula

Ana yawan samun rahotannin yadda batagarin matasa ke kwacen wayoyin bayin Allah a Kano.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta tashi tsaye wajen yaki da matsalar gadan-gadan.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya ce na’urar da gwamna Ganduje ya siyawa rundunar ta na matukar taimakawa a bangaren tsaro.

Ƴansanda a Kano sun shiga farautar ɓarayin waya wanda hakan yayi sanadiyyar damƙe har guda sittin 60 daga cikinsu, ka na kuma sun gano ɗaruruwan wayoyin da ƴan daba suka kwata daga hannun bayin Allh ta ƙarfin tsiya.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, C.P Habu A.Sani, wanda akafi sani da “Kalamu Wahid” shine ya sanar da hakan lokacin taron ilmantarwa da masu sana’ar sayar da waya, inda akayi musu ƙarin haske akan buƙatar haɗa hannu da jami’an tsaro don yaƙar mummunar ta’adar ƙwacen waya.

Da yake nuna godiyarsa, kwamishinan ya ce; “nau’urar bin diddigi ta miliyan ₦500 da gwamnatin mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta siyawa rundunar ‘yan sanda a Kano ya taimaka matuƙa wajen gano ɓarayin da kuma wayoyin da suka sace.

“Na’urar bin diddigin jami’an tsaron wadda ba iya mu kaɗai muke mora ba harda maƙwabtan jihohin Katsina, Jigawa, Zamfara, Sokoto da sauransu ta taimaka wajen yaƙar Fashi da makami, ta’addanci, satar mutane da sauran manyan miyagun laifuka” a cewarsa.

Kwamishina Sani(Kalamu Wahid),wanda mataimakin Kwamishina mai kula da atisayen rundunar ya wakilta,DCP Balarabe Sule,yace “Yawan samun koke koken mutane a Ɗan Agundi,Titin Obasanjo,Rijiyar Lemo,shine ya jawo hankali hukumar ƴansandan suka ɗauki matakin gaggawa inda su farwa ƴan fashin wayar ba ƙaƙƙautawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here