An Kama Ma’aikatan Gwamnati da Masu Ritaya Kan Aikata Zambar N4.8bn

 

Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta kwamushe ma’aikata bisa zargin aikata zamba kan wani aiki.

An kuma zargi wasu kamfanoni uku da hannu a lamarin, lamarin da ya kai ga fara bincike mai zurfi a kan lamarin.

Kotu ta ba da umarnin kamo dan takarar sanata a jam’iyyar APC a jihar Kano bisa zargin ya damfari wani dan kasar waje.

Jihar Oyo – Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta jihar Oyo ta kama ma’aikatan gwamnati da wasu wadanda suka yi ritaya bisa zargin zamba a aikin kwangilar N4.8bn da aka bayar a 2018.

Shugabar hukumar, Mai shari’a Eni Esan (mai ritaya) ta bayyana a cikin wata sanarwa ta ranar Laraba cewa, wasu daidaiku ne suka yi cinye kudin a karkashin hukumar gyaran tituna ta jihar, kamar yadda hukumar ta gano a wasu bayanai da ke hannunta.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu hukumar na ci gaba da tattara bayanan da suka dace don kai maganar gaba, rahoton Punch.

An tura kudi ga wasu kamfanoni 3, amma basu yi aiki ba Esan ta ce, zambar da ake zargi ta faru ne ta hanyar biyan wasu kamfanoni uku N4.8bn amma kuma basu yi aikin ba.

A yanzu haka hukumar na bin diddigin kamfanonin, hakazalika ana ci gaba da bincikar jami’an gwamnati da ke da hannu a cikin lamarin.

Hakazalika, hukumar ta nemi kamfanonin uku da su ba da bahasin kudaden da aka ce sun shiga asusun bankinsu tare da yin karin bayani.

A bangare guda, hukumar ta jaddada cewa, babu wanda yafi karfin doka, kuma tabbas doka za ta yi aiki akan wadanda ke da hannu a lamarin, Daily Sun ta ruwaito.

Ba sabon abu ne kudade su bata a hukumomin gwamnati, musamman a fannin ayyukan da suka shafi gine-gine.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here