Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Zanga-Zanga 42 a Ghana

 

‘Yan sanda a Ghana sun ce sun damke mutane 42 cikin masu zanga-zanga a Accra, babban birnin ƙasar.

Hakan ya biyo rikicin da ya faru bayan cin karo da ƴansanda da masu zanga-zangar suka yi.

Suna zanga-zangar ce domin nuna damuwa game da matsin tattalin arziki.

Tun a ranar Juma’a suka fara zanga-zangar kuma ana sa ran za su ci gaba a yau Litinin.

Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne sun yi maci a cikin birnin Accra suna wakoki tare da ɗaga kwalaye, inda suke suna damuwa kan irin ɓarnar da hako ma’adinai ta ɓarauniyar hanya ke yi wa muhalli.

Matasan kuma na ganin cewa gwamnati na almubazzaranci da kuɗaɗen da ake samu a harkar ma’aidinai.

Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta ce mutane 42 ne aka tsare kawo yanzu.

Kakakin ‘yan sandan, Grace Ansah Akrofi ta ce za a gurfanar da matasan a gaban kuliya bisa zargin kawo tsaiko a kan hanya da kuma lalata dukiyar gwamnati da kuma tayar da hankali.

A cewar ‘yan sandan, masu zanga-zangar sun saɓa doka saboda cire makullin motar ‘yan sanda tare da jefar da makullin sannan kuma sun ture shingen da jami’an tsaro suka saka.

A halin yanzu, ‘yan sandan na neman ɗaya daga cikin shugabannin masu zanga-zangar Oliver Barker Vormawor saboda laifin guje wa kame.

Sai dai jagoran masu zanga-zangar ya musanta zargin inda ya ce maganar ‘yan sandan ba ta da tushe.

A martaninta, ƙungiyar Democracy Hub wadda ke kan gaba wajen shirya wannan zanga-zangar, ta yi Alla-wadai kan yadda ‘yan sanda suka yi amfani da karfi da kuma abin da ta kira dirar mikiya kan masu zanga-zangar lumana.

Zanga-zangar na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a watan Disamba kuma batun tattalin arziki shi ne ya kankane yaƙin neman zaɓen ƙasar.

Manyan ‘yan takara biyu a zaɓen su ne mataimakin shugaban ƙasa, Mahamudu Bawumia na jam’iyyar NPP mai Mulki da kuma tsohon shugaban ƙasa, John Mahama na NDC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here