An Kama Masu Zanga-Zanga 24 a Kaduna

 

Rundunar ƴansanda a jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 23 cikin masu zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Mansur Hassan ya tabbatar wa BBC cewa wadanda aka kaman sun yi ƙoƙarin kutsawa ne zuwa cikin gidan gwamnati.

Ya kuma ce mutanen sun yi ɓarna kala-kala a lokacin zanga-zangar.

“Sun ƙona motarmu ta APC, sun ƙona babban ofishin Kastelia sun faffasa ofishin Kadipa sun kwashe kaya.”

Ya bayyana cewa dama sun samu bayanai na tsaro da suka nuna cewa wadanda ke yin zanga-zangar za su fake da ita domin aikata laifi.

Sai dai jami’in ya musanta cewa an kashe mutum ɗaya a cikin masu zanga-zangar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here