Hukuncin da Kotu ta Yanke wa Tsohon Ministan Sufurin Singapore Kan Karɓar Kyaututtuka

 

Kotu a Singapore ta yanke hukuncin ɗaurin shekara ɗaya ga tsohon ministan sufurin ƙasar Subramanian Iswaran bisa samunsa da laifin rashawa da yi wa shari’a karan-tsaye – shi ne mutum na farko tsoho ko minista mai ci da aka ɗaure a ƙasar.

Iswaran mai shekara 62 ya amsa tuhume-tuhume biyar da aka gabatar a kansa a makon da ya gabata, ciki har da batun karɓar kyaututuka da kuɗaɗensu ya haura dala dubu 300.

Wakiliyar BBC ta ce bincike ya nuna cewa ya karɓi kyaututtuka daga manyan mutane da ƴan kasuwa da suka haɗa da tiketin zama kyauta a otel, tafiye-tafiye da wasu tarukan sharholiya.

Masu gabatar da ƙara sun nemi a kulle shi na tsawon wata shida zuwa bakwai, amma masu kare shi sun nemi mako 8.

Wannan shari’a ta Iswaran ta girgiza siyasar Singapore da ake mata kallon mai tsafta a idon duniya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here