Hukumar OCRITIS ta kama Masu Safarar Miyagun ƙwayoyi a Damagaram
Hukumar yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi ta Jamhuriyar Nijar OCRITIS, ta ce ta kama mugayen ƙwayoyi a wani yanki na jahar Damagaram da ke kan iyaka da Najeriya.
OCRITIS ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta yi a yau Litinin a Yamai.
Hukumar ta gabatar wa manema labarai wasu mutum uku ne dukkan su ƴan Nijar a matsayin wadanda aka kama da sama da kilo 100 na tabar wiwi, da kuɗi da wayoyin hannu damota da sauransu.
Hukumar Ocritis ta ce ta yi nasarar bankaɗo wannan gungun na ƙasa da ƙasada ya shahara wajen fataucin miyagun ƙwayoyin bisa ƙwarewa da kuma jajircewar jami’anta.
Read Also:
Mataimakiyar babban mai shigar da ƙara na ƙasa Mme Maidamma Hadizatou ta cewannan gungun yana aiki ne tsakanin kasashen Najeriya da Togo da Benin da Ghana da kuma Nijar.
Gungun kan yada zango a Nijar ne kasancewar akwai masu sha da dama inda sauran kuma ake zarcewa da ita ƙasashen ketare.
Sannan ta kokawa kan yadda jahar Damagaram ke neman zama sabon yankin fataucin ƙwaya daga Najeriya zuwa cikin Nijar domin ƙetarawa da ita ƙasashen waje.
Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da ta ba su goyon baya wajen daƙile irin wannan yunƙuri na neman ɓatawa ko lalata tarbiyyar matasa ta hanyar sa ido da kula.
Ta ce hakan zai tabbatar wa matasan makomar kirki a gobe da kuma neman taimako wajen bankado ire-iren waɗannan gungu na masu fatauci da sai da ƙwayoyin.