An Kama Waɗanda Suka yi wa Shugaban ƙungiyar ƙwadago, Ajaero Duka

 

A ranar Laraba ne mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mal Nuhu Ribadu, ya nemi afuwar gamayyar ƙungiyar ƙwadago kan harin da aka kai wa shugabanta a Najeriya, Joe Ajaero, a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Ajaero, wanda ya je garin Owerri domin jagorantar zanga-zanga, ya sha duka tare da tsare shi na sa’o’i da dama.

Sakamakon haka, ƴan ƙwadagon suka bai wa gwamnati wa’adin biya musu wasu buƙatu da suka haɗa da kama waɗanda suka kai hari kan Ajaero, tare da yin barazanar shiga yajin aikin a faɗin ƙasar idan ba a biya musu bukatun ba.

“Sakamakon afkuwar lamarin, an umarci hukumomin da suka dace da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin,” in ji Ribadu.

Sai dai wasu rahotanni na cewa tuni an riga an kama wasu da ake zargi da hannunsu a lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com