Yadda Kamfanin Iran Yake yi wa Mutane Ta’adi – NCC 

 

Hukumar kula da sadarwa ta Najeriya tace masu kutse na kokarin damfarar mutane a Najeriya.

A wata sanarwa da ta fito a yau, NCC ta ja-kunnen jama’a game da kamfanin Iran mai suna Lyceum.

Lyceum suna yi wa mutane kutse, sun yi kaurin-suna a kasashe irinsu Saudiyya, Israila da sauransu.

Abuja – Hukumar kula da sadarwa ta kasa watau NCC, tace an kawo mata karar wata kungiyar ‘yan kutsen yanar gizo a kasar Iran mai suna Lyceum.

Jaridar Punch ta rahoto hukumar NCC tana cewa kungiyar ta Lyceum tana harin kamfanonin sadarwa da masu bada damar ziyartar shafukan yanar gizo.

Masu kutsen na neman yadda za su kai hari ga ma’aikatar kasar wajen Najeriya da na kasashen Afrika.

Rahoton yace wannan kungiya da aka fi sani da Hexane, Siamesekitten ko Spirlin yana harin kamfanonin ne da nufin su kai masu hari ta yanar gizo.

Jaridar The Eagle ta fitar da jawabin da hukumar NCC tayi a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, 2021, tana fadakar da mutane a kan sharri kungiyar Lyceum.

Nigerian Computer Emergency Response tace ayi hattara “Bayani kan harin yanar gizon ya zo cikin shawarwarin da tawagar da ke daukar matakin gaggawa.

The ngCERT yana ganin yiwuwar ta’adin yana da karfi.”

“Wannan kungiya sun yi suna wajen yi wa kamfanonin layin waya da ISPs kutse.

Tsakanin Yuli da Oktoban 2021, an samu Lyceum da kai hari a kasashen Israila, Maroko, Tunisiya, da Saudi Arabiya.” – NCC.

Yadda Lyceum yake yi wa mutane ta’adi – NCC

“Da zarar Lyceum sun yi nasarar kutsawa na’urar mutum, za su rika bibiyar al’amuransa Daga nan sai su aikowa mutum tsutsotin Shark da Milan.

NCC tace Lyceum da aka fi sani da yi wa kamfanonin gas na kasashen gabas ta tsakiya adawa, ya fara kai hari ga irin wadannan kamfanoni na sadarwa da ISP.

Idan ‘yan kutsen suka kai ga na’urorin mutane, sai su nemi kai hari ga shugabanni da manyan kamfanonin, don haka ake kira a sa ido wajen hawa yanar gizo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here