Dauko Kaya Daga China Zuwa Legas ya fi Arha a Kan Kai Kaya Daga Legas Zuwa Kano – Shugaban Kamfanin BUA
Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu, ya ce dauko kaya daga China zuwa Legas ya fi arha a kan kai kaya daga Legas zuwa Kano.
A cewar gogaggen dan kasuwan kuma hamshaƙin mai arziƙin, farfaɗo da fannin sufurin jiragen kasa ba ƙaramin abun alheri ne ba ga Najeriya.
Dan asalin jahar Kanon ya ce Najeriya danƙare ta ke da filin noma tare da albarkatu daban-daban, hakan kuwa babbar hanyar arziki ce.
Abdussamad Rabiu, shugaba kuma mamallakin kamfanin BUA, ya ce ya fi arha a dauko kwantena daga China zuwa Legas a kan daga Legas zuwa Kano.
Ya sanar da hakan ne a birnin Paris yayin da ya ke tsokaci a kan damammakin da akwai a fannin sufurin Najeriya, ballantana a fannin jiragen ƙasa, Daily Trust ta wallafa.
Rabiu ya ce saka hannun jari ballantana a fannin jiragen ƙasa zai samar da damammaki ga ƙasar da masu saka hannayen jarin.
Rabiu ya jinjinawa mulkin shugaban ƙasa Buhari a fannin inganta ɓangaren sufurin jiragen ƙasa a faɗin ƙasar.
Ya yi kira ga masu kuɗi na duniya da masu saka hannayen jari da su zuba shi a fannin sufurin jiragen ƙasa.
Read Also:
Ya ce da filaye masu matukar kyan noma a Najeriya, akwai damammaki a fannin noman abinci na siyarwa tare da haƙo ma’adanai da sarrafa su.
Kamar yadda yace, Najeriya na zaune ne a kan biliyoyin tan na albarkatun ƙasa wadanda suka haɗa da limestone wanda kamfaninsa ke amfani da shi wurin samar da siminti.
“Najeriya ta na zaune kan tan biliyan 45 na limestone kuma a halin yanzu dukkan masana’antun samar da taki a ƙasar nan su ke amfani da shi wurin samar da tan miliyan 30 na taki a kowacce rana.
“Muna iya samar da takin amfaninmu da na fitarwa ƙasashen ƙetare.
“Kamfani na kadai da ke Sokoto ya na fitar da taki zuwa jamhuriyar Nijar wacce ke da nisan kusan kilomita 120 daga kamfanin. Sannan zuwa Ouagadougou a Burkina Faso na da nisan kilomita 400 daga Sokoto.
Najeriya ta na daya daga cikin ƙasashe 12 a duniya da ke da ƙarfe, iskar gas da kwal, amma abun takaici ne yadda Najeriya ke shigo da ƙarfe.’
Daily Trust ta rawaito cewa, ya kara da cewa:
“Mu na kashe dala biliyan 2.5 a kowacce shekara wurin shigo da ƙarfe Najeriya.
“Da wannan dala biliyan 2.5 din, ya dace a ce mun iya kafa kamfanin da zai samar da ƙarfe tan miliyan ɗaya da rabi zuwa tan miliyan biyu a kowacce shekara.”