Tuwita ta Zaɓi Ghana ne Kawai Amma Kamfanin Zaifi Maida Hankali ga Najeriya – Shugaban Bankin Sterling
Shugaban Bankin Sterling ya ce yan Najeriya dakansu ne suka tura tuwita taje Ghana ta gina Hedkwatar ta na Africa saboda halinsu.
Abubakar Sulaiman ya ce masu zuba hannun jari ba zasu zuba dukiyar su a ko ina ba bayan Najeriya.
Sulaiman ya ce Tuwita ta zaɓi Ghana ne kawai amma Kamfanin zaifi maida hankali ga Najeriya.
Shugaban bankin Sterling, Abubakar Sulaiman, ya zargi yan Najeriya da laifi kan tsallake Najeriya da kamfanin tuwita ya yi wajen gina hedkwatar sa a Africa.
A kwanan nan ne dai kamfanin tuwita ya bayyana cewa zai gina hedkwatar sa a Africa a ƙasar Ghana.
Sai dai ana ganin kamfanin sada zumuntan zaifi maida hankali a Najeriya amma zai gudanar da aikinsa ne daga ƙasar Ghana.
Tuwita ta shirya ɗaukar ma’aikatan ta daga Najeriya a yarjejeniyar yin aiki daga inda suke ba dole sai sun bayyanar da gangar jikinsu ba.
Read Also:
Wannan hukunci da kamfanin tuwita ya yanke na kai ofishinsa Ghana ya baiwa mafi yawan cin yan Najeriya mamaki, inda suka ɗora alhakin hakan kan gwamnati.
Kamfanin tuwita dai ya bayyana dalilinsa na kai hedkwata Ghana. Daga cikin dalilan da daraktocin tuwita suka bayyana akwai; damar yin magana, da kuma demokaradiyya.
A wani jawabi da kamfanin ya fitar, ya ce kasancewar sakateriyar kasuwancin Africa na Ghana, shine ya ƙara ma kamfanin kwarin gwuiwar ya tsallake Najeriya.
Duk da waɗannn dalilan da kamfanin ya faɗa, Abubakar Suleiman, ya na ganin laifin yan Najeriya ne.
Ya ce munanan kalaman da yan Najeriya ke yi wajen misalta ƙasar su yasa tuwita tsallake ta wajen gina hedkwatar a Africa.
Ya ce yan Najeriya suyi dai tsammanin komai makamancin wannan saboda yadda suka ɓata ƙasar a idon masu zuba hannun jari. Suleiman yace: “Da farko kun faɗawa duniya Najeriya cike take da abun tsoro, sannan kunji Tuwita zata gina hedkwata a Ghana Kuma kuna mamakin meyasa haka.
Idan har ba zaka iya siyar da kanka ba, babu wanda zai siya.” “Har yau-Har gobe Najeriya itace zuciyar Nahiyar Africa, duk ƙalubalen da muke fuskanta ba dawwamamme bane.”