Mutane 14 sun Mutu, 886 Sun Kamu da Cutar Kwalara a Najeriya – NCDC
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya, NCDC ta ce kimanin mutane 14 suka rasa rayukansu sakamakon cutar kwalara a tsawon mako biyar, a ƙasar.
Wani rahoton da hukumar ta fitar kan cutar a ranar Talata ya nuna cewa akalla mutane 886 aka yi tunanin sun kamu da cutar a tsakanin 27 ga watan Janairun shekarar 2025 zuwa biyu ga watan Fabairun da ya gabata.
Rahoton ya ƙara da cewa an samu ɓullar cutar a jihohi 22 na ƙasar, lamarin da ya shafi ƙananan hukumomi 44.
Read Also:
Hukumar ta ce jihar Bayelsa da ke kudancin ƙasar, ta bayar da rahoton zaton mutane 695 sun kamu da cutar ta amai da gudawa.
Sai jihar Rivers da ke biye da ita da mutane 54, yayin da jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar, ta bayar da rahoton zargin mutane 33 sun kamu da cutar.
A cewar rahoton, jihohin Sokoto, Yobe, Borno, Katsina, Borno da Adamawa na cikin jihohin da aka samu mutum guda kacal da aka yi zaton sun kamu da cutar a tsawon wannan lokaci.
Sai dai hukumar ta ce an samu ƙaruwar cutar amai da gudawar a bana, idan aka kwatanta da daidai lokacin a bara, inda aka samu 506.
Hukumar ta bai wa al’umma shawarar shan ruwa mai tsafta, wanke hannu da sabulu, cin abincin da aka dafa sosai da tabbatar da tsaftar muhalli domin kaucewa kamuwa da cutar ta kwalara.