ALLAH ya yi wa ‘Dan Shirin Kannywood, Ahmad Tage Rasuwa

 

Rahotannin da BBC ke samu na tabbatar da rasuwar tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ahmad Tage.

Kafin rasuwarsa ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, har ta kai ga an kwantar da shi a asibitin Nasarawa da ke jahar Kano.

Tuni ‘yan wasan Hausa na Kannywood suka fara mika ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta.

Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro.

‘Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 21.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here